An Fallasa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) A Matsayin Mai Sayan Makaman HKI

Rahotanni sun bayyana gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa a matsayin kasa ta farko wacce take sayan makaman HKI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta

Rahotanni sun bayyana gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa a matsayin kasa ta farko wacce take sayan makaman HKI.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan fallasar ta zo ne a dai dai lokacinbda kungiyoyin kare hakkin bil’adana a duniya suka zargin HKI da aikata kisan kiyashi da laifukan yaki a Gaza.

Kafin haka dai kamfanin kera makamai na HKI Elbit Systems ya bada sanarwan kulla kontaragin sayan makamai wadanda kimarsa ya kai dalar Amurka biliyon $2.3 wanda kuma zai mikasu ga kasar da ta saya a cikin shekaru 8, amma bai ambaci kasar ba. Sai dai daga baya bincike ya tabbatar da cewa Abu Dhabi ce.

Kafin haka dai ana zargin Hadaddiyar daular Larabawa da tallafawa yan tawayen kasar Sudan RSF da makamai wadanda suka aikata ayyukan ta’addanci da su a yankin Darfur na yammacin kasar.

Banda haka a wani labara wakilin MDD kan abubuwan da suke faruwa a kasar Falasdinu Francesca Albanese ta shaidawa Majalisar kan cewa kasashe kimani 60 a duniya wadanda suka hada da kasashen Turai da Amurka da kuma wasu kasashen musulmi da larabawa ne suke taimakawa HKI don ta ci gaba da kissan kiyashin da take yi a Gaza tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Wadannan kasashe sun kulla wata yarjeniyar da HKI na shimfida layin dogo daga kasar Indiya wanda zai ratsa ta kasashen UAE saudiya da kuma Jordan har zuwa Haifa a cikin HKI. Banda haka wadan nan kasashe suna hulda da HKI a bangarori da dama a asirce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted