Bayan tsaiko na tsawon shekaru 9, an dawo da zirga-zirgar jiragen saman a tsakanin Iran da Saudiyya, inda wani jirgi daga Mashhad ya tashi, ya sauka a Dammam a gabashin Saudiyya.
Wadanda su ka halarci saukar jirgin na kamfanin “ Homa” na Jamhuriyar musulinci ta Iran a can kasar Saudiyya sun hada da jakadan Iran a Riyadh, sai kuma wakilan hukumar jiragen sama ta kasar Saudiyya.
Ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran dake Riyahd ya sanar da cewa daga yanzu an bude Zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin kasashen biyu, bayan da cibiyoyin sufuri na kasashen su ka dauki dukkanin matakan da su ka dace na ganin hakan ta faru.
Ma’aikatar sufuri ta sanar da cewa; A yau Talata ne aka dawo da zirga-zirgar jiragen saman a tsakanin Mashahad zuwa Dammam wacce kamfanin jirgin sama na “ Homa” na Iran ya bude. Bugu da kari a kowane mako a ranakun Talata da Alhamis jirgin zai rika zuwa Saudiyya.
Birnin Dammam yana a gabashin Saudiyya ne kuma shi ne cibiyar gundumar gabashin kasar da take a gabar ruwan tekun Pasha.