Mahukunta a kasar Benin sun kama da daure tsohon ministan tsaro kasar Candide Azannai a karkashin binciken da ake yin a yunkurin juyin mulkin da bai kai ga yin nasara ba a farkon wannan watan na Disamba.
Azannai dai shi ne shugaban jam’iyyar adawa, yana fuskantar tuhumar kitsawa gwamnati makarkashiya, da kuma yin tunzura domin ayi bore.
A makon da ya shude ne dai aka kama shi a ofishin jam’iyyar tasa a birnin Cotonou, tare da tsayar da shi a gaban kotun dake shari’ar laifuka masu alaka da tattalin arziki da kuma ta’addanci. Kotun ta bayar da umarnin a tsare shi na wasu sa’o’i domin ya asma tambayoyi.
A gefe daya mahukunta a kasar ta Benin sun sanar da kama wasu sojoji biyar saboda Rashin tseguntawa gwamnati abinda yake faruwa. An kuma kama wasu gwamman sojojin da ake tuhuma da laifukan “Cin Amnar Kasa.”, Kisan gilla’ da yi wa gwamnatin barazana ta tsaro.
A ranar 7 ga watan Disamba ne wasu sojojin kasar su ka bayyana a tashar talabijin din kasar ta Benin, suna sanar da kifar da gwamnatin Patrice Taloon.
Sai dai ba a je ko’ina ba,mahukuntan kasar su ka sanar da dakile kokarin juyin mulkin bisa taimakon Nigeria da Faransa.
Sai dai kuma yunkurin juyin mulkin ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada sojoji, yayin da ake ci gaba da neman wasu ruwa a jallo daga cikinsu har da wanda ya jagoranci juyin mulkin Pascal Tigry.