Hukumar da take fada da ‘ta’addanci a Najeriya, ta sanar da daure mutane 30 da aka samu da laifin taimaka wa kungiyar Boko Haram da kudade,yayin da aka dage shari’ar wasu 10 zuwa wani lokaci anan gaba.
An yi zaman shariar ne dai a wasu kotuna 4 na musamman da aka kafa, a cikin barikin soja na Kanji a Jahar Niger.
Mai Magana da yawun kotun ya ce, hukuncin da aka yankewa mutane ya kama a tsakanin zaman shekaru 10 zuwa 30, tare da aiki mai tsanani.
Tun daga shekarar 2017 ne ake yi wa masu alaka da kungiyar Boko Haram hukunci a Nigeria, da ya zuwa yanzu an yi wa mutanen da sun kai 785 hukunci.
Kungiyar Boko Haram ta shelanta fada a Nigeria tun a shekarar 2002, wanda ya zuwa yanzu ta ci rayuka masu yawa a cikin kasar da kuma kasashen makwabta da su ka hada Nijar, Chadi, da Kamaru.
Daga cikin salon fadan da kungiyar take amfani da su da akwai harin kunar bakin wake, jefa bama-bamai da kuma kai hari kai tsaye da bindigogi.
A 2014 ne dai kungiyar ta Boko Haram ta sace dalibai mata a makarantar kwana ta Chibok su 276, tare da kone ginin makarantar.
Makarantun Boko da dama dai sun fuskanci hare-hare daga kungiyar ta Boko Haram a tsawon wannan lokacin.