Yau Litini 16 ga watan Satumba, shekara guda cif da kafa kawancen kasashen AES, da ya hada kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar.
A rana irin ta yau ce a shekarar 2023, Shugabannin kasashen uku suka sanya hannu kan yarjejeniyar kulla kawancen na tsaro da tattalin arziki a tsakaninsu.
Sun kulla yarjejeniyar ce a ranar Asabar 16 ga watan Satumba a Bamako babban birnin kasar Mali.
“A ranar shugabannin kasashen Burkina Faso da Nijar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar Liptako-Gourma da ta kafa Kawancen Kasashen Sahel, wato Alliance of Sahel States (AES), wanda zai tattaro bayanai kan sha’anin tsaro da taimaka wa dukkan al’ummominmu”, in ji shugaban kasar Mali, Assimi Goita, a lokacin.
Yankin Liptako-Gourma – inda kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka yi iyaka da juna – ya dade yana fama da matsalolin hare-haren masu tayar da kayar baya.
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tiani ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai cike da ”tarihi” yana mai cewa “dukkanmu za mu gina al’ummar yankin Sahel mai cike da zaman lafiya da tsaro da hadin kai.”
Kasashen sun kafa kungiyar a yayin da dukkansu suka shiga takun tsaka da ECOWAS, wacce tuni suka fice daga cikinta sakamakon takkadamar data biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, inda kungiyar ta yi barazanar amfani da karfin soji.
Kasashen uku duka sun zargi Ecowas, da zama ‘yar amshin shatan kasashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka.