An Bukaci Majalisar Dokokin Espaniya Ta Goyi Bayan Katse Huldar Jakadanci  Da HKI

Kwamitin da aka kafa a kasar Espaniya don gabatar da matakan da gwamnatin kasar zata dauka kan HKI, ya bukaci majalisar dokokin kasar ta goyi

Kwamitin da aka kafa a kasar Espaniya don gabatar da matakan da gwamnatin kasar zata dauka kan HKI, ya bukaci majalisar dokokin kasar ta goyi bayan shawarar katse hulda da HKI sanadiyyar laifuffukan yakin da take aikatawa a Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta na cewa kwamitin ya kunshi lawyoyi, masu rajin kare hakkin bil’adama alkalai, masu gabatar da kara, da malaman jami’o’i.

Kakakin kwamitin Mai sharia Pilar Barrado yana bayyana cewa mambobin kwamitinsa kimani mutum 1000 guda ne, sun bukaci kasar Aspania ta mutunta dokokin kasa da kasa wadanda suka hada da kotun kasa da kasa ta ICJ,da kuma kwamitin tsaro na MDD.

Pilar Barrado ya ce su na goyon bayan kasar Espaniya ta katse huldar jakadanci da HKI, ta katse huldar kasuwanci da ita, ta kuma kafawa wasu jami’an gwamnatin kasar wadanda suke da hannu dumu-dumu a cikin kissan kare dangi a gaza takunkuman tattalin arziki.

Kwamitin ya bukaci majalisar dokokin kasar Espania ta goyi bayan duk bukatun da kwamitinsa ya gabatar don sauke nauyin da ke kantt kan Falasdinawa wadanda ake kashesu duk ranar All..

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments