An Bude Wuta Akan Ofishin Jakadancin “Isra’ila”  Dake Kasar Jordan

Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa a safiyar yau Lahadi ce aka  kaiwa ofishin jakadancinsu dake kasar  Jordan hari da bindiga, kuma tuni jami’an

Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa a safiyar yau Lahadi ce aka  kaiwa ofishin jakadancinsu dake kasar  Jordan hari da bindiga, kuma tuni jami’an tsaro sun rufe hanyar da take isa ofishin da ke birnin Amman.

Wani mutum ne dauke da bindiga ya kai hari a kan ofishin jakadancin, wanda daga karshe ya yi taho mu gama da jami’an tsaron kasar ta Jordan masu tsaron wurin, inda tuni suka kashe shi.

 Jami’an tsaron kasar ta Jordan sun bayyana cewa 3 daga cikinsu sun jikkata.

Kafin haka dai an ji jami’an tsaron suna yin kira da amsa-amo ga mazauna unguwar da su zauna a cikin gidajensu, a daidai lokacin da suke neman mutumin da ya kai harin, amma daga baya sun gano shi sun kuma kasashe shi.

Kafafen watsa labarun kasar ta Jordan sun bayyana cewa jami’an tsaro sun killace hanyoyin da suke isa zuwa ofishin jakadancin na Haramtacciyar kasar Isra’ila dake birnin Amma.

Har ila yau an ga motocin daukar marasa lafiya sun nufi unguwar “Rabiya” inda ofishin jakadancin HKI yake, a birnin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments