An bude taron sauyin yanayi na Afrika karo na biyu

An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi

An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi a nahiyar.

Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha suka shirya, na samun halartar wakilai 25,000 da kuma shugabannin kasashe 45.

Haka kuma, taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa.

Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron.

Bankin raya kasashen Afirka ya yi kiyasin cewa ana bukatar dala biliyan 100 a duk shekara domin daidaita ababen more rayuwa, da tsaron aikin gona, da zuba jari a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a Afirka.

Sai dai a cewar wani rahoton sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, dala biliyan 30 ne kawai aka tara wa Afirka tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024 ta asusun kula da yanayi na Green Climate (GCF).

A cewar Mahamoud Ali Youssouf, shugaban hukumar ta AU, “kasashen Afirka na bukatar garanti mai karfi da sabbin hanyoyin samar da kudade don sauya burinsu zuwa ayyuka na zahiri.”

Bisa takardar share fagen taron, Afirka na bukatar kusan dala biliyan 579 don samar da kudaden da za ta samar da daidaita tsakanin shekarar 2020 zuwa 2030.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted