A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna juyayi ga jaririn Imam Hussain ( a.s) Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala.
Iyaye mata dauke da kananan yaransu masu watanni 6 daga haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran suna masu mika juyayinsu na shugaban Shahidai Imam Hussain ( A.S).
Bugu da kari iyaye matan sun gargadi HKI da Amurka akan fada da Iran, suna masu cewa; Dukkanin ‘ya’yansu da za su girma za su kasance sojojin Imamul Hujja ( a.s) da za su yake su.
Baya ga Iran da akwai kwasu kasashe 45 da ake juyayin Ashura a duniya.
Taro mafi girma na juyayin Ashuda din shi ne na hubbaren Imam Riza ( a.s) dake birnin Mashhad. Adadin wuraren na juyayin Ashura na kananan yara sun kai 700 a cikin birane da kauyukan Iran.