Bayanai daga Isra’ila na cewa an harbe mutum shida a wani hari da aka kai a birnin Tel Aviv.
Akalla wasu mutane bakwai kuma sun jikkata, da dama daga cikinsu sun samu munanan raunuka.
‘Yan sanda sun ce harin ya auku ne a kusa da tashar jirgin kasa da ke yankin Jaffa na birnin.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce maharan biyu da aka gani suna sauka daga jirgin kasa, wani mai wucewa ne da kuma wani mai gadi ne suka harbe su.