Tarayyar turai ta bakin wata kwamishiyarta Hadja Lahbid wacce ta kai Ziyara a yankin Goma dake gabashin DRC, ta bayyana cewa; yanayin da ake ciki na yaki da cewa, ya yi muni, tare da yin kira da a kai wa yankin dauki na agaji da gaggawa.
Kwamishinar tarayyar turai da samar da daidaito a tsakanin al’umma ta kuma ce da akwai bukatar a wayar da kai akan bukatuwa da aikewa da kayan agaji zuwa yankin.
Wannan ne karon farko da tawagar tarayyar turai ta kai Ziyara zuwa yankin na Goma tana mai yin gargadin cewa; “Ana ci gaba da take dokokin kasa da kasa masu alaka da ayyukan agaji.”
Daga cikin wuraren da ta kai wa ziyarar da akwai asibitoci, ofisoshin jami’an gwamnati, sannan kuma babban birnin kasar, Kinshasa,inda ta gana da shugaban kasa Felix Tshikedi.
A birnin Goma ta gana da wakilan kungiyoyin tawaye da suka shimifida ikonsu a cikin yankin, wato M23 da kumaAFC, inda ta yi kira da su bude tattaunawa da gwamnati domin shimfida zaman lafiya.