An Ayyana Dokar Ta-baci A Wasu Yankunan Siriya

Gwamnatin Syria ta ayyana dokar ta-baci a yankuna da dama na kasar bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke

Gwamnatin Syria ta ayyana dokar ta-baci a yankuna da dama na kasar bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke kara murkushe fararen hula.

An sanya dokar ta-baci a birnin Tartus da ke arewa maso yammacin kasar da kuma daukacin lardin Homs a daren Alhamis.

An kuma sanar da dokar hana fita a Latakia har zuwa karfe 10:00 na safe agogon kasar ranar Juma’a.

Dokar hana fita ta biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Alawiyyawa da mabiya Shi’a suka yi, wadanda suka yi Allah wadai da ta’addancin gwamnatin.

Sun zargi gwamnatin rikon kwarya ta Syria da fifita mulki kan sake gina al’ummar kasar.

Majalisar koli ta addinin musulunci ta Alawite a kasar Syria ta fitar da wata sanarwa, inda ta yi tir da karuwar tashe-tashen hankulan da gwamnatin kasar ke yi, da suka hada da kai hare-hare ta sama kan gidajen fararen hula da tilastawa mazauna su kauracewa gidajensu.

Sanarwar ta yi kira ga al’ummar Syria da su gudanar da zaman lumana tare da kauracewa barnatar da dukiya ko kuma shiga rikicin kabilanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments