Amurka Zata Yanke Tallafin Dala Biliyan 4 Da Ake Ba Wa Isra’ila

shugaban Amurka zai dakatar da tallafin biliyan 4 da take bawa isra'ila a karshen shekara ta 2026

Shugaban kasar Amurka Donald trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta yanke kudi dala biliyan 4 na talallafin da take bawa isra’ila a karshen shekara ta 2026 da muke ciki, yace an dauki matakin ne sakamakon suka da yan jam’iyar Demucrat suke yi da sauran yan hamayya game da ci gaba da taimakon kudi da Amurka take bawa gwamnatin isra’ila

Shugaban Amurka ya bayyanawa tashar fox news cewa shi  da fira minister isra’ila benjemen Natanhayo sun cimma matsaya a bari wahington ta kawo karshen tallafin da take bawa isra’ila a karshen wannan shekara ta 2026,

Yace tuni mun amince cewa zuwa karshen wannan shekara ba zamu sake biyan gwamantin isra’ila ba, amma yanzu zamu iya taimaka mata idan tana bukata, sai dai har yanzu natanyaho da gwamnatin isra’ila basu ce komai ba game da lamarin

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin isra’ila ke tattaunawa da Amurka kan samun tallafi daga Washington bayan shekara ta 2028, lokacin da yarjejeniyar  samar da taimakon soja daga Amurka zuwa isra’ila za ta kare

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted