Yemen Ta Jawowa Saudia Asarar Dalar Triliyon $2

Chas Freeman, tsohon jakadan kasar Amurka a Saudia ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin Huthawa na kasar yemen sun jawowa kasar Saudia asarar dukiya

Chas Freeman, tsohon jakadan kasar Amurka a Saudia ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin Huthawa na kasar yemen sun jawowa kasar Saudia asarar dukiya wacce ta kai dalar Amurka trillion $2. Ya kuma tabbatar da cewa saudia ba zata sami nasara a wannan yakin ba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na gwamnatin kasar Iran ya nakalto tsohon jakadan yana cewa, a wannan fasalin sanyi kasashen turai da dama zasu yi ta fama da sanyi saboda rashin gas wanda zasu dumama gidaje da ofisoshi da kuma kamfanoninsu, saboda yakin da Amurka ta dorawa JMI.

Ya ce, a bangaren tsaro kuma daga yanzun kuma kasar Amurka ba zata ci gaba da ajiye sojojinta a kasashen yankin yammacin Asiya ba, saboda kasashen basa bukatarsu bayan yakin da Amurka ta dorawa JMI kumata yi amfani da kasashen don yin hakan, wanda ya zama masu musiba babba.

Yace idan yakin nan ta kawo karshen babu sojojin Amurka da zai rage a cikin kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted