Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka ta ce adadin mutaten da suka mutu a harin wata motar daukar kaya a yankin New Orleans ya kai 15.
‘Yan sandan New Orleans sun ce an kashe wanda ake zargin ne bayan ya yi musayar wuta da ‘yan sanda tare da yunkurin guduwa.
Hukumar ta FBI ta tabbatar da gano wanda ake zargi da kai harin mai suna Shamsud-Din Jabbar, mai shekaru 42, wanda wani tsohon jami’in sojan Amurka ne.
A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an gano tutar kungiyar IS a cikin motar wanda ke nuni da cewa harin na ta’addanci ne.
Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a ranar Laraba cewa hukumar FBI ta sanar da shi cewa wanda ake zargin ya yada bidiyoyi a shafukan sada zumunta da ke da alaka da ta’addanci.
Haka zalika shugaba Biden ya kuma ce hukumomi na gudanar da bincike kan wata fashewar data auku a mai masaba da motar Tesla Cybertruck a wajen wani otal mallakar zababben shugaban kasar Donald Trump a Las Vegas a ranar Laraba.