Ma’aikatar Tsoron Amurka ta Pentagon ta fitar da sabbin alkaluma game da mutuwar sojojin Amurka a harin da ta kai wa Iran
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta (Pentagon) ta ƙara yawan hasarar da ta yi na sojojinta a yakin da suka da Iran ta hanyar ba da ɗimbin ƙididdiga da bayanai.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr kamar yadda ta nakalto daga jaridar Washington Post ta bayyana cewa: Ma’aikatar Tsaeon Amurka ta Pentagon ta yi ikrarin cewa: Adadin sojojinta da aka kashe a harin da suka kai kan Iran ya fi na yawan na baya da aka bayyana.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ƙara da ƙarin sojojin sama biyu a cikin rumbun adana bayanai, wanda hakan ya ƙara adadin sojojin Amurka da aka kashe a hari kan Iran zuwa 23.
Ma’aikatar Tsaron ta Amurka ta yi ƙaryar cewa: Dukkan sojojin saman biyu sun mutu ne a cikin abubuwan da aka ayyana a matsayin hatsari da ba na yaƙi ba.
Rundunar Sojan Sama ta Amurka ta yi iƙirarin cewa: Daya daga cikinsu ya mutu ne sakamakon rashin lafiya, yayin da ba a sanar da musabbabin mutuwar na biyun ba tukuna kuma har yanzu ana kan bincike.