Rundunar Sojojin Amurka (AFRICOM) ta sanar da cewa ta tura wani rukunin sojoji a tarayyar Najeriya.
Wannan sanarwar ta zo ne bayan hare-haren sama da Amurka ta kai kwanan baya a Najeriya.
Janar Dagvin R.M. Anderson ya nuna cewa wannan tura sojoji ya biyo bayan wani taro da shugaban Najeriya Bola Tinubu a Rome a karshen 2025, inda ya nuna cewa ana bukatar karin dabaru don magance “barazanar ta’addanci a Yammacin Afirka.”
A watan Disamba, Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da izinin kai hare-hare Najeriya, bis azargin gwamnatin Najeriya da rashin tabaka komai wajen kare al’ummarta Kiristoci, batun da gwamnatin Najeriya ta sha musantawa.