Amurka ta sanya takunkumi kan mutane 16 da kuma wasu kamfanoni 10 da ke da alaƙa da Iran
Gwamnatin Amurka ta ci gaba da ayyukanta na bangare guda da kuma na haramtacciyar hanya ta ƙara mutane 16 da ƙungiyoyi 10 da ke da alaƙa da Iran cikin jerin sunayen waɗanda aka sanya wa takunkumi.
Kamfanin dillancin labaran Mehr, wanda ya ambato daga kiamfanin dillancin labaran Reuters, ya ruwaito cewa: Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da sabbin takunkumin da suka shafi Iran kan mutane 16 da ƙungiyoyi 10.
A cewar wani rahoto a shafin yanar gizon Ma’aikatar Baitulmalin Amurka, gwamnatin Trump ta sanya sabbin takunkumi kan Iran a ranar Alhamis, 15 ga Oktoban wannan shekara ta 2026.
Sanarwar ba ta bayar da ƙarin bayani game da asalin mutane da ƙungiyoyin da takunkumin ya shafa ko takamaiman dalilan da suka sa aka ɗauki matakin ba.
Wannan matakin ci gaba ne na manufofin takunkumin gwamnatin Amurka kan Iran.
A cikin ‘yan watannin nan, gwamnatin Amurka ta faɗaɗa takunkumin da ta sanya wa Iran don haɗawa da ɓangarorin kuɗi, man fetur, sufuri da kayan aikin soja.