Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni.
Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, bayan da ya dade yana adawa da kasancewar Amurka a can.
Amurka dai ta shafe shekaru da dama tana da sojoji a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke yaki da ISIS.
A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Sean Parnell ya fitar, ya ce za a rage yawan dakarun Amurka a Siriya zuwa kasa da dakaru 1,000 a cikin watanni masu zuwa daga kusan 2,000.