Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya Ambato wasu jami’an kasar Amurka suna fada a jiya Lahadi cewa, sun kwace wani jirgin dakon man fetur na kasar Venezuela a gabar Ruwan wannan kasa, da shi ne na uku a cikin kasa da mako daya.
Sai dai jami’an gwamnatin Amurka da su ka yi magana da kamfanin dillancin labarun na “Reuters’ ba su bayyana sunan jirgin Ruwan na dakon mai din da aka kwace ba.
Sai dai kuma wasu majiyoyin sun ce jirgin Ruwan da aka kawace shi ne: Villa 1 wanda yake dauke da tutar kasar Panama, kuma yana kan hanyarsa ne ta zuwa Venezuela domin daukar man fetur.
A ranar Asabar din da ta gabata ma dai Amurkan ta kwace wani jirgin Ruwan dakon man fetur na Venezuela, mai suna “Sentoshoriz” sai kuma wani jirgin Ruwan mai suna: Skyper” a ranar 10 ga watan Disamba.
Amurka dai ta kafa wa kasar ta Venezuela takunkumin man fetur, wanda ba ya bisa doka. Haka nan kuma ta kira yi shugaban kasar Nocholay Maduro da ya sauka daga kan kujerar Mulki,ko kuma ta yi amfani da karfin soja wajen kifar da shi.
Donald Trump na Amurka dai ya zargi Venezuela da cewa tana shigar da muggan kwayoyi zuwa cikin Amurka, lamarin da gwamnatin Caracas ta karyata.
Veneuzuela ta zargi Amurka da fashi da makamashi akan doron ruwa saboda kwace mata jiragen Ruwan dakon man fetur. Haka nan kuma gwamnatin ta kasar ta ce, abinda Amurkan take yi ba zai wuce ba tare da ta fuskanci sakamako ba.