Amurka ta sanar da kakaba wasu sabbin takunkumai kan Iran wanda ya shafi wasu mutane da kuma wasu cibiyoyi da ta ke zargin suna da alaka da shirye-shiryen sojan Iran da ke da nufin kerawa da samar da jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami na Iran.
Gabadaya, mutane uku da cibiyoyi hudu, ciki har da na wajen Iran, takunkumin ya shafa.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa takunkunim ya shafi mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgediya Janar Majid Mousavi wanda ta ce yake da hannu a ayyukan da suka ba da gudummawa ga shirin makamai masu linzami na Iran.
Har ila yau, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya takunkumi kan wasu hukumomi biyu, wadanda ba a bayyana sunayensu ba, wadanda ta ce sun taimaka wa Iran wajen kera jiragen yakin samfarin Shaheed-136.
Amurka ta sake nanata zargin da ta yi a baya na cewa Iran ta ba wa Rasha jiragen yakin Shaheed-136 don yin amfani da su a yakin da take da Ukraine.
Iran dai ta sha yin watsi da zargin cewa ta bai wa Rasha makaman da za ta yi amfani da su a yakin na Ukraine.