Amurka Ta Kakabawa Ma’aikatar Tsaron Rwanda Takunkumi

Amurka ta ce Rwanda ta kasa cika alkawarin da ta doka a karkashin Yarjejeniyar Washington.

Amurka ta sanar da sanya wa ma’aikatar tsaron Rwanda takunkumi bisa zarginta da goyon bayan ‘yan tawayen M23 a DRC, kamar yadda Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar a ranar Laraba.

Matakin na zuwa ne ‘yan watanni kadan bayan da Washington ta sanya wa sojojin Rwanda takunkumi.

Takunkumin a cewar Amurka ya shafi Ma’aikatar Tsaro ta Rwanda da kuma kamfanin Zigama, wata cibiyar kudi ga membobin jami’an tsaron kasar.

 “Dole ne Rwanda ta dakatar da goyon bayanta ga M23 ta kuma janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo,” in ji Sakataren Baitulmalin Amurka Scott Bessent a cikin wata sanarwa.

Amurka ta ce Rwanda ta kasa cika alkawarin da ta doka a karkashin Yarjejeniyar Washington, in ji Bessent.

Saboda haka, duk kadarorinsu da muradunsu a Amurka an daskare su.

A cewar Scott Bessent, wadannan matakan suna da nufin aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin Rwanda da Congo suka sanya wa hannu a watan Disamba da ya gabata, karkashin jagorancin Washington. Yarjejeniyar da Donald Trump ke yawan alfahari da ita.

A cewar Washington, dubban sojojin Rwanda suna fafatawa tare da ‘yan tawayen M23 a gabashin DRC.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted