Amurka Ta Kai Hari A Najeriya Da Sunan Yaki Da Daesh

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kaddamar da harin soji a Najeriya da sunan abin da ya kira yaki da Daesh. Wannan na

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da kaddamar da harin soji a Najeriya da sunan abin da ya kira yaki da Daesh.

Wannan na zuwa ne dai bayan da a kwanakin baya shugaban na Amurka ya yi da’awar cewa ana yi wa kiristoci kisan gilla a Najeriya, kuma ya yi barazanar cewa zai dauki matakin soji a kan hakan.

A nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar da labarin, inda ta ce Amurka tab kaddamar da hare-haren a daren wannan Juma’a a kan wasu sansanoni na mayakan Daesh a wasu yankuna da ke arewa masu ymmacin kasar.

Najeriy ace kasa mafi girma ta fuskar yawan jama’a da tattalin arziki, sannan kuma tana fuskatar matsaloli na tsaro daga ‘yan ta’adda tsawon shekaru, wanda wasu suke Kallon harin na Amurka a wannan lokaci da sunan yaki da ta’addanci yana tattare da alamomin tambaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted