Gwamnatin kasar Amurka ta basa sanarwar jingine mafim yawan bukatun Visa na shiga kasar daga kasar Zimbanwe, tare da bayyana damuwar gwamnatin Amurka da sabawa sharuddan bada visar musamman wuce lokacinda yakamata a fice daga kasar.
Majiyar ofishin jakadancin Amurka a birnin Harare ta bayyana cewa wannan bay a nuna cewa Amurka ta daina bada Visar shiga Amurka kwata-kwata ba. Sai dai dakatarwa na wani lokaci ne, sannan ko a yanzun zata bada visa ga jami’an diblomasiyya da wasu al-amuran da ake iya bada Visar. Sai mafi yawan visar diblomasiyya da wasu bukatun gwamnatin kasar.
Kafin haka gwamnatin kasar ta Amurka ta takaita yawan Visar da take bayarwa na shiga Amurka daga Zimbabwe, sannan a wannan karon an kusan jingine bada Visar ga sauran mutane sai zuwa abinda hali yayi.
Labarin ya kammala da cewa kashi 10.57 % na yawan yan kasar Zimbawe wadanda suka wuce lokacinda da aka kayyada masu na zama a cikin Amurka a shekara ta 2023. Sannan a wani labarin kuma, a kasashen Malawi da Zambiam ana bukatar wasu wadanda suke bukatar Visa zuwa Amurka sai sun aje kudade akalla $15,000
Wasu sun nbayyana wannan zai shafi wadanda mutanen musamman wadanda suke da iyalai a kasar ta Amurka.