Amurka Ta Hana Wakilin Falasdinawa Halartar Babban Taron MDD

kasar Amurka ta hana wakilan falasdinawa visar shiga amurka don halartar babban taron majalisar dinkin duniya

Kungiyar gwagwarmaya ta hamas ta yi tir da matakin da Washington ta dauka na hana bada visa ga wakilan falasdinawa shiga Amurka don halartar babban taron majalisar dinkin duniya karo na 81 a birnin newyork kuma ta bayyana matakin a matsayin keta yarjejeniyar da jagororin majalisar dinkin duniya suka amince da ita,

Kakakin kungiyar Hamas Hamzem Qassem yace wannan mataki ba mataki ne na saniyar ware ba, wani bangaren na tsarin Amurka dake na nuna goyon bayan isra’ila ido rufe game da ci gaba da mamaye yankin falasdinu da take yi.

Wannan yin Alla wadai  yana zuwa ne bayan da kasar Amurka ta sanar cewa Washington za ta kara tsawaita takaita bada visa ga jami’an hukumar falasdinu da mambobin kungiyar kwato falasdinu ta plo,

Hani shi ne karo na biyu a jere , inda a shekara ta 2025 ma kasar Amurka ta hana visa ga mahamud abbas shugaban gwamnatin falasdinu da sauran jami’ai, kuma suka tilastawa abbas ya gudanar da jawabinsa ga babban taron mdd ta hanyar bideyo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted