Amurka Ta Dakatar Da Shirin Hadin Gwiwa Da Kasar Jojiya, Bisa Zargin Kusanci Da Rasha

Amurka ta sanar da dakatar da wani shirin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Jojiya bisa zarginta da neman kara kusanci da kasar Rasha. Matakin dai

Amurka ta sanar da dakatar da wani shirin hadin gwiwa tsakaninta da kasar Jojiya bisa zarginta da neman kara kusanci da kasar Rasha.

Matakin dai na zuwa ne bayan da Jojiya ta yanke shawarar dakatar da shawarwari kan yiwuwar shiga Tarayyar Turai, abin Amurkar ta kira, da karkata zuwa ga Rasha, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya sanar a kan shafin X, jiya Asabar.

Ya kuma yi ikirarin cewa matakin da jam’iyyar ta dauka “cin amana” ne ga kundin tsarin mulkin kasar ta Turai.

A ranar Alhamis data gabata ce firaministan Jojiya, Irakli Kobakhidze, ya sanar da dakatar da shirin shiga kasar a tarayyar Turai, tare da bayyana cewa kungiyar ta EU, na jiran Georgia data aiwatar da wasu sauye-sauye kafin a amince da ita, wanda kuma kasar ta Jojiya ta bayyana a matsayin keta mutuncin kasar.

Jami’in na magana ne kan bukatu daban-daban na Brussels kan Tbilisi, ciki har da soke dokar wakilan kasashen waje da ta bukaci kungiyoyi masu zaman kansu da kafofin watsa labarai da ke karbar sama da kashi 20 na kudadensu daga masu ba da agaji na kasashen waje don yin rajista a matsayin kungiyoyi “

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments