Amurka ta ce a shirye take ta koma tattaunawa da Iran

Majiyoyin diflomasiyyar kasashen yamma sun shaidawa tashar Al Mayadeen cewa, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Switzerland Gabriel Luginger ya aike da sako daga manzon Amurka

Majiyoyin diflomasiyyar kasashen yamma sun shaidawa tashar Al Mayadeen cewa, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Switzerland Gabriel Luginger ya aike da sako daga manzon Amurka Steve Witkoff ga jami’an gwamnatin Iran a Tehran.

A cewar majiyoyin, sakon na Witkoff ya nuna cewa a shirye Washington ta ke ta sake komawa tattaunawa tare da Iran, da kuma ba da tabbacin cewa babu wani rikici da zai barke a yayin da suka koma tattaunawa.

Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa Tehran ta samu sakon daga Witkoff, wanda ya bukaci a koma tattaunawa kan batun Shirin Iran na nukiliya.

A farkon wannan wata, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce ba a yanke wani abu ba tukuna dangane da tattaunawar nukiliyar Iran da Amurka, ya kara da cewa har yanzu ba a tabbatar da kasar da za ta daukin nauyin karbar bakuncin taron ba.

Da yake magana a gefen taron majalisar ministocin kasar, Araghchi ya kuma yi jawabi game da wata Ziyara da jami’an  hukumar ta IAEA za su yi a Tehran, inda ya bayyana cewa mataimakin darakta janar na hukumar zai sake komawa Tehran.

Araghchi ya fayyace cewa “babu wani shiri na ziyartar duk wani bangare na tashar nukiliya kafin cimma matsaya da aka amince da ita,” yana mai jaddada cewa “wannan tsarin zai kasance bisa dokar majalisar dokokin kasar ne kawai” kuma “ba za a fara duk wani shiri na hadin gwiwa kafin cimma wata matsaya ba.”

Kasar Iran dai ta fice daga tattaunawar da take yi da Amurka ne bayan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila tare da taimakon Amurka suka kai hari kan shirinta na nukiliya, inda Amurka ta jefa bama-bamai a wasu muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran din  a yankuna da dama na kasar, biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai kan manyan jami’an tsaro da na nukiliya na kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fayyace a cikin watan Yuni cewa Iran ba ta ga wani dalili na yin cudanya da wata hukuma da ke goyon bayan ayyukan soji na gwamnatin sahyoniyawa a kan Iran ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments