Search
Close this search box.

Amurka Ta Bukaci A Kai Zuciya Nesa Yayin Da Iran Ke Shirin Ramuwar Gayya

A daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata kan martanin da Iran za ta mayar kan kisan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismael da

A daidai lokacin da hankalin duniya ya karkata kan martanin da Iran za ta mayar kan kisan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismael da Isra’ila ta yi a Tehran, Amurka ta Bukaci a kai zuciya nesa, a kuma lalubo hanyar tsahaita wuta a Gaza kamar yadda aka faro.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga Tehran da Tel Aviv su amince da tsagaita wuta Gaza domin “karya lagon yakin” da ke faruwa.

“Ƙara aukawa cikin yaki ba zai yi wa kowa dadi ba, Zai haddasa karin yaki da tarzoma da rashin tsaro ne kawai, Yana da muhimmanci mu karya lagon wannan yakin ta hanyar amincewa da tsagaita wuta a Gaza,” in ji Blinken a hira da manema labarai.

Blinken ya yi kiran ne a yayin da ake cikin zaman dardar kan yiwuwar hare-haren da Iran da kawayenta za su kai wa Isra’ila domin yin martani kan kisan shugaban Hamas da kwadandan Hezbollah a makonnin da suka gabata.

An bayyana cewa shugaban Amurka Joe Biden, wanda kasarsa ta aike da jiragen ruwan yaki da manyan makakai yankin Gabas ta Tsakiya, yana shirin gudanar da taro mai muhimmanci da shugabannin tsaron kasarsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments