Dubban masu adawa da siyasar Donald Trump na Amurka ne su ka yi gangami a kusa da “Central Park” dake birnin Newyork, sannan su ka nufi hasumiyar Trump dake cikin birnin.
Dubban mutanen dai suna nun kin amincewarsu ne da kisan da wani jami’in ‘yan sanda ya yi wa wata mace wacce ‘yar hijira ce mai suna Ranee Good.
Haka nan kuma masu gangamin sun bayar da taken kin amincewa da siyasar shugaban kasar akan ‘yan hijira.
An gudandar da wannan irin Zanga-zanga a cikin garuruwa da biranen kasar ta Amurka masu yawa da su ka hada Los Angeles da Philadelphia.
A ranar juma’ar da ta gabata ‘yan sanda sun kama mutane 20 dake Zanga-zangar a Minneapolis da a can ne aka kashe matar.
A Philiadelphia masu zanga-zanga sun yi kira da a janye jami’an tsaro da suke farautar ‘yan hijira.
Jami’an tsaron na Amurka suna fuskantar suka akan kisan matar da ma amfani da karfi da suke yi.
Jami’an gwamnatin Amurka da su ka hada da shugaban kasa da mataimakinsa sun kasance na gaba-gaba wajen kare abinda ‘yan sandan su ka yi, da hakan ya mayar da su cikin wadanda masu Zanga-zanga suke suka.