Bayanai daga AMurka na cewa ana kara fuskantar mummunan yanayin kadawar iska daga kudancin gabar tekun jihar California, birnin Los Angeles na sake shirin tunkarar bazuwar wutar daji da tuni ta kone sassan daban daban na birnin.
Har zuwa jiya Litinin, dubban ’yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar da ta mamaye gundumar Los Angeles, yayin da wutar dajin ke barazana ga karin sassan birnin tun tashinta yau mako guda.
Alkaluman da hukumomi suka fitar na cewa, ya zuwa ranar Litinin gobarar wadda yanayin bushewar itatuwa da iska mai karfi ta ruruta, ta riga ta lakume sama da eka 40,500, tare da kone gine-gine sama da 12,300.
A kalla mutane 25 aka tabbatar da mutuwarsu, baya ga wasu sama da 10 da ba a san yanayin da suke ciki ba, sakamakon bazuwar gobarar a sassan Los Angeles.
Babban jami’in ’yan sanda na gundumar Robert Luna, ya shaidawa manema labarai cewa, an wajabtawa kusan mutane 92,000 kauracewa gidajensu, yayin da kuma aka baiwa wasu karin mutanen 89,000 shawarar barin yankin.