Jami’an na gwamnatin Biden guda biyu sun ce Isra’ila ta tattara isassun sojoji a gefen birnin Rafah domin kaddamar da wani gagarumin farmaki a cikin kwanaki masu zuwa.
Sai dai jami’an ba su da tabbacin ko sojojin Isra’ila za su ci gaba da kai farmaki ta kasa bayan da Biden ya yi gargadin cewa zai hana jigilar makamai zuwa Isra’ila idan har za su dauki wannan matakin.
Jami’an da CNN ta nakalto wadanda ba a bayyana sunayensu ba sun kara da cewa Isra’ila ba ta yi wani shiri ba na kwashe jama’a a Rafah kafin duk wani hari, kamar “samar da ababen more rayuwa da suka shafi abinci, tsafta da matsuguni”.
Bayanai daga yankin sun ce kusan mutane 450,000 ne aka tilastawa tserewa daga Rafah tun daga ranar 6 ga watan Mayu, lokacin da sojojin Isra’ila suka fara jibge sojoji a kusa da birnin, tare da kwace mashigar kan iyaka, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA).
“Mutane sun tsorata sosai,” in ji UNRWA a cikin wata sanarwa a kan X. “Babu inda yake da aminci, Tsagaita bude wuta nan take shine kawai abun fata”.