Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta sanar da safiyar yau Juma’a cewa, jiragen yakin Amurka da Birtaniya sun kai hari a gundumar Harf Sufyan na kasar Yemen da ke lardin Amran da ke arewacin birnin Sanaa.
Harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da rundunar sojin Yaman ta sanar da cewa dakarunta sun harba ,akamai masu linzami dad a jiragen yaki marasa matuka a kan jirgin ruwan Amurka USS Harry S.
Har ila yau wannan sabon harin na zuwa ne kwanaki biyu bayan sanarwar tsagaita wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin “Isra’ila” da ‘yan gwagwarmayar Falasdinu a Gaza.
Tun da farko gwamnatin kasar Yemen a birnin San’a ta gargadi Amurka, da Birtaniya, da mamayar Isra’ila, da dukkan makiya kasar Yemen, kan duk wani mataki na ramuwar gayya ko makarkashiyar da ake kullawa kasar Yemen, tare da shan alwashin tunkarar duk wani yunkuri na yin shishigi a kan kasar.
Hare-haren dakarun na yemen dai na zuwa ne domin nuna goyon bayansu ga al’ummar gaza da Isra’ila tare da taimakon Amurka suke yi musu kisan kiyashi tsawon watanni fiyee da 15 a jere, inda suka kashe dubban farren hula mata da kannan yara da tsoffi.