Amurka ce za ta girbi sakamakon duk wani hari da aka kai wa Iran_Araghchi

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sake nanata cewa Amurka za ta girbi cikakken sakamakon duk wani hari da aka kai wa Iran, yana

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sake nanata cewa Amurka za ta girbi cikakken sakamakon duk wani hari da aka kai wa Iran, yana mai gargadin cewa Jamhuriyar Musulunci ba za ta yi jinkirin daukar fansa ba.

Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aike wa takwarorinsa na duniya a ranar Talata, a matsayin martani ga barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kwanan nan na daukar karin matakan soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ministan harkokin wajen Iran ya yi tini da sakamakon yakin kawancen Isra’ila da Amurka da suka yi da Iran a watan Yuni, wanda sojojin Iran suka mayar da martani, yana mai jaddada cewa sakamakon duk wani hari da aka kai wa Iran zai “kare” ne kawai ga Amurka.”

Mista Araghchi ya yi gargadi game da barazanar Trump, wadda ke nuna manufofin Washington na rashin bin doka da oda, yana mai bayyana su a matsayin karya dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya haramta duk wata barazana ko amfani da ƙarfi ga yanki da na ƙasashe.

Saboda haka, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su yi Allah wadai da waɗannan kalamai masu cike da barazana a fili na shugaban Amurka akan Iran.

Mista Araghchi ya yi Allah wadai da goyon bayan Washington ga gwamnatin Tel Aviv, wanda ya ce ya jefa tsaron yanki da na duniya cikin hadari sosai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted