Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta shiga jerin mutane da kungiyoyi masu kira ga Isra’ila da ta saki Hussam Abu Safia, darektan asibitin Kamal Adwan.
A cikin wata sanarwa data fitar a shafin X, Amnesty ta ce “ta damu matuka da” makomar Abu Safia kuma “dole ne a sake shi ba tare da wani sharadi ba”.
Amnesty ta kuma yi kira ga Isra’ila da ta saki duk Falasdinawa da aka kama ba bisa ka’ida ba tare da lura da cewa “Isra’ila na tsare daruruwan ma’aikatan kiwon lafiyar Falasdinu daga Gaza ba tare da tuhuma ko shari’a ba”.
“An gallazawa ma’aikatan lafiya azaba da sauran muggan laifuka kuma ana tsare da su a gidan yari.” Inji rahoton na Amnesty.
Tunda farko dama dangin Abu Safiya sunyi kira ga duniya da ta matsa wa Isra’ila lamba ta saki Darektan Asibitin na Kamal Adwan babban asibitin karshe da ya daina aiki a Gaza sakamakon farmakin Isra’ila wanda ya ruhuza duk wani tsarin aikin asibitin.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matukar damuwa game da farmakin Isra’ila kan asibitin wanda ta ce ayyukan sun tsaya cik.