Morocco ta yi gargadin ci gaba da ambaliyar ruwa, tare da kiran jama’a da su guji komawa yankunan
Ambaliyar ruwa ta ci gaba da mamaye biranen Morocco da dama, wanda hakan ya sa hukumomi suka gargaɗi mazauna yankunan da su guji komawa yankunan da abin ya shafa.
A safiyar Juma’a, Ma’aikatar Cikin Gida ta Morocco ta yi kira ga ‘yan ƙasar da su kasance masu taka tsantsan tare da gujewa komawa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa har sai yanayi ya inganta. Ma’aikatar ta yi gargaɗi game da ci gaba da haɗarin ruwa da kuma rashin wata alama da ke nuna cewa ambaliyar ruwan tana raguwa.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar ta ce bayanai game da halin da ake ciki akwai hasashen munantan yanayi da ya nuna yiwuwar taɓarɓarewar lamarin da kuma ƙaruwar matakin haɗari, idan aka yi la’akari da ci gaba da kwararar ruwa da kuma cikan madatsun ruwa.
Ma’aikatar ta kuma fitar da wani bidiyo da ke nuna ƙaruwar matakan ruwa a birnin Ksar El Kebir na arewacin ƙasar, sakamakon ƙaruwar kwararar ruwa daga Kogin Loukkos.