Alummar Falasdinu Sun yi Tir Da Isra’ila Na Iko Da wurare Musulmi

ma'aikatar da wuraren tarihi na falasdinu ya yi tir da kokarin kwace ikon kula da wurare masu tsarki na musulmi

Ma’aikatar kula da kadarorin Addini ta falasdinu tayi tir da matakin da gwamnatin isra’ila ke son dauka na mayar da kula da wurare masu tsarki na musulumi karkashin ikonta, a wani bangaren na shirinta na fadada ikonta a yankin baki daya

Ma’aikatar ta bayyana mataki a matsayin wani shiri na isra’ila na kwace muhimman wurare a yankin ya koma karkashinta domin ci gaba da fadada  shirinta na gine-ginen matsugunan yahudawa yan share wuri zauna,

Don haka ta yi kira ga hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa da ta shiga tsakanin don datar da keta alfarmar  wuraren girmamawa na musulmi a yankin falsdinu da kuma kare yankunan musulmi da kayayyakinsu daga babakeren isra’ila

A watan fabareru isra’ila ta fadada ikon jamian binciken kayan tarihi da ya kunshi wasu matakai da ya hade da gefen wuraren tarihi dake yankin da ke karkashin ikon gwamnatin falasdinnu kamar yadda hukumar Emerk shaveh ta bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted