Al’ummar Chadi Na Zaben ‘Yan Majalisar Dokoki

Al’ummar kasar Chadi za su zabi ‘yan majalisar dokoki a kasar a yau Lahadi. Shugaban mulkin soji, Mahamat Idriss Deby ya ce zaben wani bangare

Al’ummar kasar Chadi za su zabi ‘yan majalisar dokoki a kasar a yau Lahadi.

Shugaban mulkin soji, Mahamat Idriss Deby ya ce zaben wani bangare ne na kawo karshen wa’adin shirin mika mulki na shekara uku da aka yi bayan rasuwar mahaifinsa.

Saidai ‘yan adawa sun yi kira ga al’ummar kasar su kaurace wa zaben, bayan da suka yi zargin cewa Mista Deby na da niyyar yin amfani da zaben don karfafa ikonsa.

A ranar Asabar Sojojin Chadi da makiyaya sun kada kuri’a a babban zaben.

Mahamat Deby mai shekaru 40 ya karbi mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar ta yankin Sahel.

Mahamta ya lashe zaben shugaban kasa na shekaru biyar a watan Mayun da ya gabata.

Tun shekarar 2011 ba a sake zaben ‘yan majalisa ba a kasar, sanadin matsalolin kudi da na tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments