A yau ne al’ummar kasar Brazil suka sake fita ƙaɗa kuri’ar a zagaye na biyu na zaɓen shugaban kasa da ake fafata tsakanin shugaba mai ci Lula da Silva da ke neman wa’adi na hudu a kan mulkin da Flavio Bolsonaro dan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro wanda ya jagoranci kasar tsakanin shekara 2019 zuwa 2023.
A zagayen farko, dan takarar na jam’iyyar masu zazzafar ra’ayi ya baiwa abokin karawarsa Lula da Silva tazarar maki biyu inda ya samu kashi 47% na yawon kuri’un da aka kada.
Zaɓen na Yau lahadi ya nada matukar muhimmanci saboda yazo daidai lokacin da Amurka ke shirin gudanar da zaben rabin wa’adin mulki ranar 3 ga Nuwamba gobe.
Masu kada kuri’a a Brazil sun fita runfunan zaben ne don yanke hukunci tsakanin mutane biyu masu mabambanta manufofi.