Aljeriya ta sanar da zama mamba a sabon bankin raya kasashe na BRICS, ta manyan kasashe masu tasowa.
A ranar Asabar din da ta gabata ne kwamitin gwamnonin NBD karkashin jagorancin tsohuwar shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ya amince da shigar Aljeriya bankin a yayin taron shekara na wannan hukuma karo na 9 a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.
Kungiyar BRICS ta kirkiri Bankin na NDB, a shekarar 2015, a matsayin bankin raya kasashe da aka tsara a matsayin kishiya wa bankin bada lamani na duniya (IMF) da Bankin Duniya.
Ta hanyar shiga “wannan muhimmin bankin, na kungiyar BRICS data hada (Brazil, Rasha, Indiya, Sin, Afirka ta Kudu), Aljeriya ta dauki wani babban mataki a cikin tsarinta na hada-hadar kudi na duniya”, in ji ta.
Kasancewa a cikin bankin NDB, a cewar ma’aikatar kudi ta Aljeriya, zai baiwa kasar da ke kan gaba wajen fitar da iskar gas a Afirka, ” karfafa ci gaban tattalin arzikinta “.
Aljeriya ta bukaci shiga kungiyar ta Brics amma ba a amince da bukatar ta a 2023 ba.
Amma kungitar ta amince da shigar kasashen Masar, Habasha, Saudiyya, Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Argentina da ta janye bayan zaben Javier Milei a matsayin shugaban kasar.