Ouattara Na Kasar Ivory Coast Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83  ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban. Mutum

Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83  ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban.

Mutum na biyu wanda yake bin Outara a baya shi ne tsohon ministan kasuwanci Jean-Lous Billon da kaso 3%, sai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar Simone Gbango da ta sami kaso 2.4%.

Tuni dai Billon ya taya Ouattara murnar cin zaben, bayan da ya yarda ya sha kaye.

Tare da cewa  a karkashin shugabancin Ouattara kasar ta Ivory Coast ta sami ci gaban tattalin arziki, sai dai masu bin diddigin siyasar kasar suna yin suka akan wasa da tsarin mulkin kasar domin bayar da damar ci gaba da tsayawa takarar Alassan Ouarrata.

A zaben da ya dora Alassan Ouattara kan Kargar Mulki, kasar ta fuskanci rikice-rikice na siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments