Shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yaman ya yaba da nasarar da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta samu kan Isra’ila.
Abdul-Malik al-Houthi ya fada jiya Alhamis cewa: Nasarar da Lebanon ta samu a wannan muhimmin mataki na tunkarar makiya Isra’ila wata baiwa ce daga Allah, kuma ta zo ne bayan wani matakin da ba a taba ganin irinsa ba na wuce gona da iri kan al’ummar kasar da Hizbullah.
A daya bangare shugaban kungiyar da aka fi sani da ta ‘Yan Houthi a Yemen ya ce za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu.
Abdel-Malik al-Houthi ya fada a tashar talabijin ta Al Masirah cewa: “Ayyukan da ake yi daga gaban Yaman na tallafawa al’ummar Falasdinawa da makamai masu linzami da jirage marasa matuka zuwa ga makiya Isra’ila zasu ci gaba da gudana.”
Ya kara da cewa “Mu a fagen yakin Yemen muna yin iya bakin kokarinmu don tallafawa al’ummar Falasdinu.”
‘Yan Houthi dai na kai hare-hare kan Isra’ila lokaci-lokaci da jirage marasa matuka da makamai masu linzami tun bayan barkewar yakin Gaza.
Sun kuma kai hari kan jiragen ruwa da ke da alaka da Isra’ila da wasu jiragen ruwa a cikin Tekun Maliya.