Shugaban majalisar mulkin sojin kasar Sudan Janar Abdel Fattah al Burhan ya bayyana cewa ‘yan mulkin-mallaka ne suke kara rura wutar duk wani rikici a Afirka.
Al Burhan ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a Bissau.
Al Burhan da Embalo sun gudanar da wani taron koli na kasashen biyu da zummar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasashen da kuma hanyoyin inganta hadin-gwiwa.
Janar Al’Burhan ya ce a halin da ake ciki yanzu, Afirka ta farka, kuma hakan ya ba da damar yin adawa da tsoma bakin kasashen waje a harkokin da suka shafi nahiyar.
Muna yaba kokarin wasu kasashen Afirka, wadanda suka yi tsayin daka wajen adawa da mulkin-mallaka zamanin baya da na yanzu.”
A ranar Lahadi ne dai shugaba Al Burhan ya isa kasar Guinea-Bissau, kasa ta biyu a rangadin da yake yi a Afirka, wanda ya fara daga Mali a ranar Asabar kana ana sa rai zai je Saliyo da Senegal a nan gaba.