09-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Al-adu da ci gaban addini addinin musulunci a tarihi, wanda ni tahir amin yake kawo mako sau guda a ko wani mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun tsaya inda muke magana dangane da matsayin ilmi a addinin musulunci. Inda muka bayyana cewa malaman addinin musulunci, musamman a lokacin da ake kira karnin zinari har ma zuwa lokacinda daular ta fara ja da baya, tana faduwa.
Mun bayyana cewa malaman addinin da dama sun zama masu assasa harsashen ilmin zamani da dama, kuma mun amfaci sunayen wasu daga cikinsu, wadanda kuma suna hada da Abu Ali Sina, wanda ya kware a ilmin falsafa kuma har ya rubuta littafi a kan, wato littafin Ashifaa, sannan yak ware a ilmin likitanci shi ma ya rubuta littafi a kansa wanda ake kira ‘Kanun’. Abu Ali Sina yana daga cikin likitocin da suka fara kirkiro kayakin aikin tiyata a duniya, wanda har yanzun ana amfani da fahintarsa a wannan bangaren.
Mun ambaci Jabir dan Hayyan wanda ya gani ilmi da dama a fannin chemestry, wato kimiyar sinadarai, kuma shi ne ya gano salfuric Acid a karon farko a duniya. Mohammad dan Musa khawarizmi, da muhammad dan Zakariya Razi, da Farabi da Ibn haitham, da ibnu Rushdi da wasu da dama, duk malaman addini ne suka kuma kware a ilmomin dabi’a ko ilmin zamani daban daban kafin samuwar kasashen yamma.
Da haka kuma muka tabbatar da cewa, addinin musulunci yana daular ilmin dabi’a a matsayin wani ilmi wanda ba za’a iya raba shi da ilmin addini ba. Gaskiyas al-amarin ilmin dabi’a ayoyi ne daga cikin ayoyin All..don haka suma bangare ne wanda yake kai mumini ga sanin All..da kuma daukaka shi.
Don haka a zamanin wadan nan malaman da muka ambata, an kafa cibiyoyin ilmi da dakunan karatu da kuma ajiye littafai wato Library. Da kuma wurare gwaje gwajen ilmin kamar na hangen sararin samani da ayyukan likitanci da sauransu.
Saboda haka ne Aya. Shahid Muttahari a bincikensa na Ilmi da Imani, ya yi watsi da ra’ayin kiristoci a zamanin duhu a kasashen turai na cewa, babu ruwan addini da binciken ilmi, kuma suna ganin cewa ilmin addinin suna hannun riga da ilmin dabi’a. Suna ganin imani yana hannun riga da ilmin zamani, basa haduwa ko kadan. Wannan shi ne halin turawa kafin ci gaban da suka samu a ilmin zamani wanda basu kai gareshi ba, sai da suka yi watsi da All..da kuma addinin kiristanci suka kaskanta malaman addinin kirista kafin su kai ga inda suka kai.
Aya. Muttahari yana cewa dole ne musulmi ya nisanta kansa daga fahinta da kuma kuskuren kiristoci dangane da Imani da kuma ilmi, kuma a wajemmu babu sabani tsakanin imani da ilmi, sai ma, ilmi yana karfafa imani da addini da kuma samuwar lahira da wuta da aljanna ne.
A wani bangare Aya. Muttahiri yana cewa ilmi da imani suna kammala juna ne, kuma suna taimakawa wajen maida mutum cikekken mutum a duniya da lahira. Don haka a musulunci ilmi da addini ko ilmin zamani da Imani suna tafiya tare suna taimakwa juna wajen gina mutum mumini.
A cikin alkur’ani mai girma kalmar ilmi (seince) ya zo har sau 80 a wurare daban daban a cikinsa.
Don babu shakka a addinin musulunci, kalman ilmi tana da matsayi na musamman kuma tana da matukar muhimmanci a wajensa.
All..T yana fada a cikin aya ta 11 a cikin suratul Mujadalah {..Kuma All..yana daukaka wadanda suka yi imani daga cikinku, sannan wadanda aka bawa ilmi kuma suna da darajoji…} All..T yana kira ga wayayyun mutane masu hikima su yi tunani a cikin halitun All..kama daga kawukansu zuwa taurari zuwa tsirrai zuwa duwasu, zuwa dare da rana, saboda su gane cewa akwai wanda ya haliccesu kuma yake kula da samuwarsu da wanzuwarsu a inda suka da kuma yanda suke.
Wasu ayoyin Al-Kur’ani mai girma suna kira ga musulmi su yi tunani, su zurfafa shi a cikin halittunsa kamar taurari da lissafi da sauransu saboda akwai ayoyinsu masu yawa a cikin su.
A cikin suratu Yunus aya ta biyar All..T yana cewa, {Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, mai samar da haske, da watã mai daukar haske, kuma Ya sanya shi matakai, dõmin ku san ƙidãyar shẽkaru da lissãfi. Allah bai halicci wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani.} Yunus 05.
A cikin wasu ayotin kuma, da hadisan Manzon All..(s) da limamai masu tsari, sun bayyana darajar ma’abuta sani da ilmi sosai.
Wata rana daya daga cikin sahabban Manzon All..(s) ya zo wajensa yana cewa: Ya Manzon All…(s), wanne daga ciki ya fi soyowa a gareka? Halartar jana’iza ko taron ilmi? Sai yace: Wasu mutane su halarci jana’iza don binne mamaci ya wadatar, amma halatar majalisin wani malami ya fi soyuwa a gare ni. Ka san cewa, halartar rakiyar jana’iza sau dubu, ziyartar marasa lafiya sau dubu, sallar darare dubu, azumi ranaku dubu, bada sadaka ga mabuci da miskini sau dubu, zuwan hajji dakin All..sau dubu, jihadi kan tafarkin All..tare da rai da dukiya sau dubu, gaba day aba zasu taba zama dai dai da halartar majalisar masani ba. Shin ka san cewa, ba wanda zai iya bautawa All…T ya kuma yi biyayya a gareshi ba, sai tare da ilmi?.
Alkhairin duniya da lahira yana cikin ilmi. Kuma sharrin duniya da lahira yana cikin jahilci.
A zamanin rayuwar limamai masu tsarki daga iyalan gidan Manzon All..(s), musamman a zamamin Imam Ja’afar dan Mohammad Assadik (a), sun bunkasa ilmi da ilmantarwa. Sun kuma kodaitar da karatu da karantarwa.
Imam Jaafar Assadik (a) yana cewa: Wanda y afara wani aiki ba tare da sani ko fahintarsa ba, kamar wanda ya kama hanya ba ta asali ba. Duk kara tafiya da yake yi, yana kara nisa daga daga hanyar gaskiya ne.
Don haka tarin ayoyin Alkur’ani da kuma hadisai wadanda muka kawu, da wadanda bamu kawo ba, sun tabbatar da cewa, babu wani bambanci tsakanin Musulunci da Ilmi, sannan fiye da haka suna luzumtar juna, basa sabawa.
Bugu da kari, abinda ya tabbata a tarihin ci gaban addinin musulunci, a karnukan da suka gabata, malaman ilmomi daban daban na dabi’a ko asasin ilmin zamani suna daukar nema da bincike a cikin su, nau’I ne na bautar All..suna kuma fatan samun lada daga ubangijinsu kan aikin na su.
Banda haka, malaman da suke nema kuma su bunkasa ilmomin dabi’a malamai ne wadanda suka yi zurfi a ilmin sanin akidu da tarbiyar musulunci.
An nakalto Sharafuddin Khurasani a cikin littafinsa mai suna ‘Da’iratul Ma’arif Islami’ yana fada, dangane da Abu Ali Sani, sanennen malamin falsafa kuma likita yana fada a cikin tarihin rayuwarsa kan cewa, a duk lokacinda ya rikice ya kasa fahintar wata matsala a ilmin mandiki, yakan tashi ya je masallaci, ya yi sallah raka’oii biyu sannan ya roki All..T ya fahintar da shi abinda ya shige masa duk a cikin matsalar da bai fahinta ba.
Wani abu mai muhimmanci wanda yakamata kowa ya sani dangane da addinin musulunci, da neman ilmi, shi ne, yana da sharudda. Daga cikin sharuddan, akwai cewa, ilmi da halaye masu kyau da bautar All..suna tafiya tare. Duk malamin addini ko malamin ilmin dabi’a wanda bai da halaye masu kyau bai da wani matsayi a wajen All..T, kuma ilminsa da bautarsa basu da wani amfani.
Wannan al-amarin yana da daga cikin abinda ya bambanta addinin musulunci da sauran addinai. Kuma ya Fifita shi a kansu.
A yanzun kuma bari mu fara bincike kan yanda gano rubutu da littafi ya taimaka ko kuma yayi tasiri a wajen ci gaban musulmi bayan bayyanar addinin musulunci. Wani daga ciki malaman kasashen yamma, wadanda suka yi rubutu dangane da musulmi da kasashen musulmi mai suna Hewkandi, ya bayyana muhimmancin gano takardan rubutu wajen kawo ci gaban addinin musulunci da musulmi.
Gano takarda, ya taimaka sosai wajen rayuwar ci gaba da kuma wayewar musulmi, ya taimaka wajen wadata da kuma nau’o’in ci gaba a cikin kasashen musulmi. Bayan bayyanar addinin musulunci littafi ko rubutu da karatu, musamman bayan an samar da takarda ya taka rawar a zo a gani wajen yada ilmi da addini a kasashen musulmi.
Sannan wani babban al-amari shi ne, mafi yawan ci gaban da aka samu a ‘karnukan zinari na tarihin addinin musulunci yana da dangantaka ta kud da kud al-kur;ani mai girma.
Wannan dangantakar ta al-kur’ani da ci gaban musulmci, da rubutu da karatu ya zama al-adarsu hatta bayan faduwar daularsu. Kuma ya zama wasila ta hada kan al-ummar musulmi.
Musulmi daga ko wace kabila yake, daga ko wace kasa yake daga ko wani jinsi yake, littafin Alkur’ani ya zama abin karatune a wajensu, ko da kuwa wasunsu basa ma fahintar abinda suke karatu. Wannan kuma ya zama wasilar hadin kai a tsakanin musulmi.
Hatta larabawa wadanda aka saukar da al-kur’ani a cikin harshensu, wani wanda ba balarabe ba yana iya fi shi korewa da kuma karatun al-kur’ani yanda ya dace.