Akrami: Rundunar Sojin Iran Ta Shirya Tsaf Don Tunkarar Makiya

Kakakin rundunar sojin Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasar sun shirya tsaf don gudanar da ayyukan riga-kafi idan wata barazana ta taso Kakakin Rundunar Sojin

Kakakin rundunar sojin Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasar sun shirya tsaf don gudanar da ayyukan riga-kafi idan wata barazana ta taso

Kakakin Rundunar Sojin Iran Birgediya Janar Mohammad Akrami Nia ya tabbatar da cewa: Dakarun Iran sun shirya tsaf don gudanar da ayyukan riga-kafi idan akwai barazana da ke tafe.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, Birgediya Janar Amir Akrami Nia, kakakin Rundunar Sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya amsa tambayar da wakilin Talabijin na Al-Alam ya yi masa game da motsin Amurka a yankin da kuma yiwuwar ci gaba da yaki, yana mai cewa: “Abin da ya tabbata shi ne cewa: Amurkawa suna ta gudanar da zirga-zirga da mu’amalar a yankin domin neman cimma munanan manufofinsu.

Dangane da barkewar yaki kuwa, rundunar sojin Iran ta yi kokarin amfani da wannan damar tsagaita wuta gaba daya, wajen sabunta shirye-shiryenta, inganta kayan aikinta, shigar da sabbin kayan aiki cikin fagen yaki, da kuma amfani da gogewa da darussa da taka koya a lokacin yakin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted