Wanda gwamnati ta gabatarwa da majalisar shawarar musulunci a matsayin wanda take son ya zama ministan tsaro, Mehrdad Akhlaqi ya gabatar da shirye-shriyen da yake son aiwatarwa a wannan ma’aikatar,tare da cewa; takunkuman da aka kakabawa Iran ba su tsayar da ci gaba da kera makamai da kayan yaki ba.
Akhlaqi wanda ya tsaya a gaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran a yau Litinin ya kuma yi bayani akan ayyukan da ya gabatar a baya tare da cewa a halin amincewa da shi a matsayin ministan tsaro zai aiwatar da ayyukan da aka dora masa cikin karfi.
Haka nan kuma ya ce; A makwanni biyu da su ka gabata ya ziyarci kwamandojin sojan Iran ya kuma tattauna abubuwan da suke son ganin ya kasance ta fuskar karfin soja, sannan ya kara da cewa; Da yardar Allah da akwai damammakin aiwatar da hakan a karkashin ma’aikatar tsaro.
Akhlaqi ya kara da cewa; Tabbas mutum day aba zai iya aiwatar da muhimman ayyuka ba, amma idan har ya zama minister to shakka babu zai yi aiki da gungun mutane masu kumajin juyi da kuma jihadi domin cimma manufofi.
Haka nan kuma Akhlaqi ya yi Ishara da muhimman batutuwa da ma’aikatar tsaro za ta Sanya a gaba a karkashinsa da suke kunshe a cikin alkaluma 16, daga cikinsu da akwai sake fasalin zubun ma’aikatar tsaro.
Da yake Magana akan ci gaba da kere-kere a karkashin ma’aikatar tsaro ya ce za a bunkasata sosai.