Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.

Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci

Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a yankin inda Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi ta hanyar kai hare-hare ta sama da kasa da kuma tana amfani da yunwa a matsayin wani makami na kisan mummuke,

hakan ya jawo damuwa sosai a mataki na kasa da kasa na irin laifukan yaki da kuma cin zarfin dan adam da Israila ke yi.

Tun watan oktoban shekara ta 2023 sojojin isr’ila sun kai hare-hare da yayi sanadiyar shahadar falasdinawa sama da 64964 tare da jikkatar sama da 165312, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi gargadin cewa kai hare-hare ta sama da kasa da HKI ke yi a yanki gaza da amfani da yunwa wajen azabatar da mutane yana barazana ga rayuwar dubban falasdinawa da hakan ya take dokokin kasa da kasa, kuma cin zarafin dana dam ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted