Afirka ta Kudu ta yi alkawarin ci gaba da shari’ar kisan kiyashi da ta shigar a gaban kotun ICJ a kan Isr’ila, duk da umurnin da Donald Trump ya bayar na katse taimakon da Amurka ke ba kasar Afirka ta Kudu saboda matakin da ta dauka kan babbar kawar Amurka.
“Babu wata dama” kan janye karar ta ICJ, ba tare da la’akari da duk wata barazana ko mataki da Trump zai dauka ba, a cewar ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Ronald Lamola, wanda ya kara da cewa, “Tsayawa a kan ka’idojinmu wani lokaci yana da sakamako, amma mun tsaya tsayin daka kan wannan batu, ganin cewa yana da muhimmanci ga duniya, da kuma bin doka da ka’ida.”
Dokar da Trump ya sanya wa hannu ta dakatar da ba da taimako ga Afirka ta Kudu, ya kuma yi alkawarin ci gaba da daukar wasu matakan domin takura kasar Afirka ta kudu kan matakin shigar da kara da ta dauka a kan Isra’ila game da batun yakin Gaza.
Afirka ta Kudu ta gabatar da karar kisan kiyashi kan “Isra’ila” a karshen shekara ta 2023 zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, inda ta bukaci kotun kasa da kasa da ta dauki matakai kan mahukuntan Isra’ila saboda karya yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ireland a hukumance ta shiga cikin shari’ar Afirka ta Kudu a watan Disamba 2024, kuma jim kadan bayan haka, Cuba ta sanar da aniyar ta na shiga cikin lamarin.