A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika dake gudana a kasar Morocco kasashen Senegal, najeriya, Masar da kuma Morocco mai masaukin baki sun samu nasarar kai wa zagayen daf da na karshe.
Senegal ta kai matakin ne sakamakon nasara a kan Mali ranar Juma’a 1-0.
Morocco kuwa ta kai matakin ne bayan lallassa Kamaru da 2-0.
Masar kuwa ta doke Ivory Coast da 3-2
Najeriya ta kai zagayen daf da karshe a Afcon, bayan da ta doke Aljeriya 2-0 a wasan kwata fainal ranar Asabar.
Ranar Laraba Masar za ta fafata da Senegal a wasan na daf da na karshe.
Najeriya za ta kara da mai masaukin baki Morocco, wadda ta fitar da Kamaru ranar Juma’a.