A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika da yanzu haka ke gudana a Morocco, DRC ta lallasa Benin da 1-0 a wasan da suka buga dazu.
Sai kuma Senegal wacce ta doke Botswana da 3-0
A jiya Litini Masar ta doke Zimbabwe da 2-1
Sai kuma Afrika ta Kudu ta doke Angola 2-1
Ranar Talata Najeriya zata fafata da Tanzania sai kuma Tunusia da Uganda
Ranar Laraba za’a karawa tsakanin Burkina Faso da Equatorial Guinea, sai kuma Aljeriya da Sudan, yayin da Ivory Coast zata yi wasanta na farko da Mozambique, daga bisani kuma Kamaru ta fafata da Gabon.