Adadin Wadanda Sukayi Shahada A Gaza Ya Kai 43,799

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ba da rahoton cewa adadin wadanda sukayi shahada a Gaza ya kai 43,799, yayin da wasu 103,601 suka jikkata tun

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ba da rahoton cewa adadin wadanda sukayi shahada a Gaza ya kai 43,799, yayin da wasu 103,601 suka jikkata tun farkon rikicin a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Adadin ya hada da wasu da sukayi shahada a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 35 da jikkata 111.

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa dama sun yi gargadi game da mummunan halin jin kai da ake ciki a Gaza.

An kwashe makonni biyar ana tashe tashen hankula a yankunan da aka yi wa kawanya, inda ake fama da kashe-kashe, da barna, da kuma gudun hijira a cewar MDD.

Rikicin da ke kara ta’azzara ya janyo tofin Allah tsine daga kasashen duniya, tare da kara yin kira da a tsagaita bude wuta da kuma kai dauki cikin gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments